Nijar ta tsawaita dokar ta baci a Tillabery da Tahoua
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kasar Nijar makwonni biyu da suka gabata ta ayyana dokar ta baci a wasu yankunan yammacin kasar dake makwabtaka da kasar Mali sakamakon hare-haren ta'addanci da masu jihadi ke ta kaiwa.
A zaman taron Ministoci na wannan mako ne ,Gwamnatin kasar ta sanar da tsawaita dokar.
A zaman taron minstocin mako, hukumomin Nijar sun sanar da tsawaita dokar ta baci a yankunan Ouallam, Ayorou, Bankilare, Abala da Banibangou dake jihar Tillabery dama wasu yankuna dake jihar Tahoua da suka hada da Tassara da Tillia.
Gani wa’adin ya zo karshe , zaman taron na Ministoci ya amince da tsawaita dokar na watani uku domin sake dawowa da zaman lafiya a wadanan yankuna da yan ta’ada ke ta kai hari dama kasha mutane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu