Somalia-Yemen

Somalia na son a binciki kisan 'yan gudun hijiranta a Teku

Shugaban kasar Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo
Shugaban kasar Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo REUTERS/Feisal Omar

Somalia ta bukaci Saudiya jagorar rundunar kawance da ke kai hare-hare a Yemen ta gudanar da bincike kan kisan ‘yan gudun hijiran kasar da aka aikata a kan teku.

Talla

Har yanzu dai babu wani cikakken bayani kan maharan da suka kashe ‘yan gudun hijira sama da 40 a cikin jirgin ruwa da ke gabar tekun Yemen.

Sai dai ana zargin ‘yan tawaye da ke yaki da gwamnatin shugaba Hadi.

A ranar Juma'ar da ta gabata aka bindige ‘yan gudun hijiran Somalia da suka hada da mata da kanana yara 42 a cikin wani jirgin ruwa da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai ta gabar tekun Yemen da ‘yan tawaye ke iko da shi.

Hukumar ‘yan gudun hijira ta Duniya ta ce akwai mutane akalla 80 da aka ceto bayan harin, inda 24 daga cikinsu ke cikin matsanancin hali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.