Majalisar Dokokin Nijar ta rantsar da wasu Kwamitocin guda 4 domin binciken gano zarge zargen da ake yi wa wasu manyan ‘yan siyasa da suka taba rike mukaman ministoci da ma wanda suke a kai, wajen yin ba daidai ba a ma’amalar da ta shafi kudade Daga cikin komitocin akwai mai binciken kudin cinikin Uranium da ake kira "Uraniumgate". Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna da Murtala Alhaji Mamuda dan majalisar dokokin daga jam’iyyar MNSD.