Najeriya

Mutane 46 aka kashe a rikicin Ile Ife

Mutane sun koma gudanar da harakokinsu na yau da kullum a Ife
Mutane sun koma gudanar da harakokinsu na yau da kullum a Ife thenation

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 46 a kazamin tashin hankalin da aka samu na kabilanci a garin Ile Ife da ke Jihar Osun. Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Jimoh Moshood ya ce sun kama mutane 38 wadanda ake zargi da hannu wajen kashe kashen.

Talla

Kusan mutane 100 suka jikkata a rikicin tsakanin Hausa da Yarabawa da ya faru a ranar 8 ga watan Maris a unguwannin Sabo da Lagere.

Rundunar ‘Yan sandan ta musanta zargin da ake yi wa wasu jami’anta da nuna goyan bayan wani bangare wajen tashin hankalin.

A baya Rundunar ‘Yan Sandan ta ce adadin bai wuce 20 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.