Najeriya

An kai hare hare a sansanin ‘Yan gudun hijira a Maiduguri

Dubban 'Yan gudun Hijira ke rayuwa a sansanin Muna a Maiduguri
Dubban 'Yan gudun Hijira ke rayuwa a sansanin Muna a Maiduguri RFIHAUSA/Awwal

An Hare Haren kunar bakin wake guda hudu a sansanin Muna da ke hanyar Gamboru a garin Maiguduri Jihar Borno, rahotanni sun ce hare haren sun kona runfunan 'Yan gudun hijirar da dama.

Talla

An kai hare haren ne a runfunan ‘yan gudun hijirar da misalin karfe 4:30 na dare, kamar yadda Jami’an da ke kula da sansanin suka tabbatar.

Sai dai babu cikakken bayani akan wadanda suka mutu sakamakon hare hare.

Dubban ‘Yan gudun hijira ne ke rayuwa a sansanin Muna, yawancinsu cikin runfunan kara da suka yi wa kansu matsuguni.

Awwal Janyau da ya ziyarci sansanin a kwanan baya a Maiduguri ya ce ‘Yan gudun hijirar Muna na fama da matsalar abinci da ruwan sha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI