Najeriya

Shugaban Kwastam zai kauracewa Majalisa

Shugaban Kwastam Hameed Ali ya ki sa Kaki a lokacin da ya ziyarci Majalisar Dattijai
Shugaban Kwastam Hameed Ali ya ki sa Kaki a lokacin da ya ziyarci Majalisar Dattijai naij.com

Shugaban hukumar kwastam a Najeriya Hameed Ali ya ce ba zai gurfana a gaban Majalisar Dattawan kasar ba, kamar yadda aka shirya saboda karar da wani ya shigar a gaban kotu.

Talla

Kanar Ali da ke takun saka da ‘yan majalisar wadanda suka ce dole sai ya sanya Tufafin hukumar kafin ta saurare shi, ya ce ba zai je Majalisar ba har sai Kotu ta yanke hukunci.

Majalisar Dattijai dai na son Shugaban na Kwastam ya gurfana gabanta domin yin cikakken bayani akan matakin tilastawa masu motoci biyan kudaden tara musamman wadanda aka shigo da su kasar ta barauniyar hanya.

Amma babban abin da ya fi daukar hankulan jama’a, shi ne yadda majalisar ta ce dole sai shugaban hukumar ta Kwastam, ya sanya kaki kafin ta saurare bayanin shi.

Masharhanta dai musamman masana shari’a da kundin tsarin mulkin Najeriya na ganin bai zama wajibi shugaban hukumar ya sanya kaki ba, don kawai zai bayyana a gaban majalisar dattawan.

Shugaban Kwastam Hameed Ali

Hameed Ali wanda tsohon soja ne, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi ne domin yakar rashawa a hukumar da Najeriya ke samun kudaden shiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.