Najeriya

Majalisa dattijai ta ki amincewa da wasu Jakadun siyasa biyu

Majalisar Dattijan Najeriya ta tabbatar da amincewa da jekadun siyasa guda 45 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a matsayin jekadun kasashe waje amma ta yi watsi da nadin mutane biyu daga cikin 47.

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Senatocin sun ki amincewa da nadin tsohon Alkali Sylvanus Nsofor daga Jihar Imo wanda ya kasa karanta taken Najeriya a lokacin da ake tantance shi da kuma Jacob Daodu daga Ondo da ake zargi da rashawa.

Rashin amincewa da mutanen biyu ya biyo bayan sakamakon rahoton da kwamitin kula da harakokin waje ya gabatar.

Mista Nsoformai shekaru 82 ya soki majalisa kan tambayarsa ya karanta taken Najeriya, inda ya bukaci su je su tambayi Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe yadda ya ke jagoranci duk da shekarunsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI