Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci karin haske dangane da wani cinikin mai

Cunkoson Masu neman Man Fetir a abun hawansu a Tarayyar Najeriya
Cunkoson Masu neman Man Fetir a abun hawansu a Tarayyar Najeriya RFI

Majalisar wakilan Najeriya ta bukaci gwamnan Babban Bankin Kasar CBN, Godwin Emefiele, da karamin ministan mai, Ibe Kachikwu, su bayyana gabatan ranar bakwai ga Watan Afrilu don mata bayani kan wasu kudadde mai da ake zargin su da karkatasu.

Talla

Kwamiti na musamman da aka kafa domin binciken wannan badakala, ya ce ana zargin wasu kamfanoni mai masu zaman kansu da karkata kudadde cinikin mai tsakani 2016-2017.

Kwamitin ya kuma bukaci sun bayyana tare da shugaban hafsan sojin ruwa, Ibok- Ete Ibas da shugaban bankin Keystone da Zenith wanda ke baiwa wadanan kamfani dalolin da suke cinikin mai dasu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.