Benin

Muhawarar yan Majalisa a Benin kan kudin tsarin mulkin kasar

Patrice Talon Shugaban Jamhuriyar Benin
Patrice Talon Shugaban Jamhuriyar Benin THIERRY CHARLIER / AFP

‘Yan Majalisar dokokin Jamhuriyar Benin sun kin amincewa da bukatar shugaban kasar Patrice Talon na yiwa kudin tsarin mulkin kasar gyara, da zai ba da daman rage wa’adin shugabancin kasar.

Talla

Akwai batun samar da wata kotu ta musaman da za ta mayar da hankali kan hukunta mayan jami’an Gwamnati da suka aikata ba dai- dai ba.

Wasu yan kasar ma su bin lamuran siyasar kasar ta Benin sun bayyana cewa da sauran aiki nan gaba.
Ya yinda wasu jam’iyoyin siyasa ma su adawa da haka suka kira magoya bayan su zuwa harabar majalisar dokokin kasar.

Karo na farko da Shugaba Patrice Talon ya soma fuskantar  adawa mafi girma daga yan kasar tun bayan zaben shi .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.