Shugaba El Beshir zai halarci taron Larabawa a Jordan
Wallafawa ranar:
Kungiyar Kare Hakin Bil Adama ta Human Rights Watch ta bukaci hukumomin kasar Jordan da su hana shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al Bashir shiga kasar ko kuma su kama shi kan zargin laifufukan yaki a Darfur.
Elise Keppler, Daraktan kungiyar ya ce barin shugaba El Bashir ya shiga kasar babban laifi ne saboda yadda kotun Duniya ke neman sa ruwa a jallo.
Shugaban na Sudan na daya daga cikin wadanda aka gayyata wajen taron shugabannin kungiyar kasashen Larabawa da za’a gudanar ranar laraba a Jordan.
Wasu kasashen a baya sun baiwa shugaban na Sudan damar sauka cikinsu ba tareda ya fuskanci matsalla ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu