Zimbabwe

Zazzabin cizon sauro ya kashe mutane 150 a Zimbabwe

Cutar zazzabin cizon sauro na barazana ga miliyoyin al'ummar nahiyar Afrika.
Cutar zazzabin cizon sauro na barazana ga miliyoyin al'ummar nahiyar Afrika. RFI

Akalla mutane 150 ne suka rasa rayukansu a cikin watanni biyu sakamakon cutar zazzabin cizon sauro ko kuma Malaria a Zimbabwe kamar yadda  alkaluman da gwamnatin kasar ta fitar yau Litinin ke cewa.

Talla

Alkaluman sun ce, akwai mutane kimanin dubu casa'in da suka kamu da cutar a cikin watanni biyu da suka gabata sakamakon ruwan sama da aka tafka a wannan shekara kamar da bakin kwarya.

Ma’aikatar lafiya a Zimbabwe ta ce an sami yawan mutanen da suka kamu da cutar ne sakamakon ambaliyar ruwa a kasar wadda ya kuma haddasa annobar cutar malaria a sassan kasar.

Mazauna yankunan kudancin kasar da al’amarin ya fi shafa sun rasa hanyar zuwa asibitoci don samun kulawar likitoci ko magunguna.

Tun daga watan Disambar bara zuwa Febrairun bana aka yi ta tafka ruwan sama a kudancin kasar.

Humumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta cigaba da yaki da cutar zazzabin cizon sauro da ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane musanman a kasashe masu tasowa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.