Benin

Ministan tsaron Benin ya yi murabus

Ministan Tsaron Jamhuriyar Benin Candide Armand-Marie Azannai ya sauka daga mukaminsa saboda sabanin da suka samu da shugaba Patrice Talon na shirin sauya kundin tsarin mulki.

Shugaban Bénin Patrice Talon ya sha alwashin takaita wa'adin shugabanci zuwa wa'adi guda
Shugaban Bénin Patrice Talon ya sha alwashin takaita wa'adin shugabanci zuwa wa'adi guda THIERRY CHARLIER / AFP
Talla

Azannai ya sanar da murabus dinsa a shafin Facebook inda ya bayyana dalilai na halin da Benin ta shiga na sauyin siyasa.

Shugaban kasar Patrice Talon ya bayyana shirin sauya kundin tsarin mulkin Benin musamman kan bukatar takaita wa’adin mulkin shugaban kasa zuwa wa’adi guda, matakin da wasu ‘yan siyasar kasar ke adawa da shi

Shirin shugaban kasar dai ya sha bambam da na shugabanin Afirka da ke sauya kundin tsarin mulki don ci gaba da zama a karagar bayan kamala wa’adin su.

Majalisar Benin dai yanzu za ta gudanar da muhawara tare da kada kuri’ar amincewa da sauya kundin tsarin mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI