Sama da yara 340,000 na fama da yunwa a Kenya - Red Cross
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kungiyar bada agaji ta Red Cross, ta yi gargadin cewa mutanen da ke bukatar agajin gaggawa wajen samun abinci a kasar Kenya sun karu zuwa miliyan 3 cikin watanni uku.
Kungiyar, ta kuma koka, bisa yadda ta ce, sama da yara 340,000 ne, ‘yan kasa da shekaru 5, basa samun abinci mai gina jiki, yayinda a gefe guda dubban dabbobi ke cigaba da mutuwa a sassan kasar saboda yunwa.
Kasar Kenya ta fada cikin tsaka mai wuyar ce, sakamakon fuskantar karancin ruwan sama a lokutan damuna sau biyu a jere, wanda hakan ya taimaka wajen samun karancin kayan amfanin gona da manoman kasar suka girbe.
Bincike ya nuna cewa a watan Fabarairun da ya gabata, farashin kayan masarufi a kasar, ya karu da kashi 9, mafi tsauri cikin shekaru 5.
Kenya, daya ce daga cikin kasashen gabashin Nahiyar Afrika da ke fuskantar karancin abinci, bayan kasashen Ethiopia, Sudan ta Kudu da kuma Somalia, inda majalisar dinkin duniya ta yi shelar suna cikin yanayi na fuskantar matsanancin fari.
Lamarin na zuwa, yayinda majalisar ta kuma bayyana kasashen Yemen da Najeriya, a matsayin wadanda suma su ke fuskantar hadarin fadawa cikin fari, abinda majalisar dinkin duniyar ta bayyana a matsayin yanayin wahala mafi muni da aka taba gani tun bayan kawo karshen yakin duniya na biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu