DR Congo

An gano gawarwakin Ma'aikatan MDD a DR Congo

Jami'an tsaro MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya a DR Congo
Jami'an tsaro MDD da ke aikin wanzar da zaman lafiya a DR Congo Photo MONUSCO/Force

An gano gawarwakin wasu kwararrun ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya biyu da aka yi garkuwa dasu a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2017,a yankin Kasai da ke DR Congo.

Talla

Mutanen biyu sun hada da BaAmurke Micheal Sharp da ‘yar asalin Sweden Zahida Catalan a yankin da ke fama ta tashe-tashen hankula.

Kakkakin gwamnatin Congo, Mista Lambert Mende, ya shaida labarin gano gawarwakin ga kafar yada labaran Faransa AFP

An dai yi garkuwa da kwararrun ne a yankin Kasai da ke tsakiyar kasar tare da wasu ‘yan asalin Congo hudu da ke rakiyarsu a wannan lokacin.

Tun a watan Augustar bara ake fama da rikici a kasai, bayan zargin dakarun gwamnati da kashe wani jagoran ‘yan tawaye mai suna Kamwina Nsapu, da ya dadde yana adawa da shugaba Joseph Kabila.

Rikicin ya ci gaba da yaduwa har zuwa wasu yankunan kasar tare da sanadi mutuwar mutane akalla 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.