Cote d’Ivoire

Kotu ta wanke Simone Gbagbo daga laifukan yaki

Wata Kotu a Cote d’Ivoire ta wanke matar tsohon shugaban kasar Simone Gbagbo daga tuhumar da ake mata na hannu wajen laifufukan yaki da cin zarafin Bil Adama.

Kotu ta wanke Simone Gbagbo daga zargin aikata laifukan yaki
Kotu ta wanke Simone Gbagbo daga zargin aikata laifukan yaki ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

An tuhumi Gbagbo da aikata wadanan laifukan a rikicin siyasar kasar da ya hallaka mutane sama da 3,000 a shekarar 2011.

Wannan ita ce shari’a ta farko da aka yi a cikin kasar na laifufukan cin zarafin Bil Adama bayan gwamnatin kasar ta ki gabatar da ita a kotun duniya.

Lauyan matar tsohuwar shugaban kasar Mathurin Dirabou ta yaba da hukuncin kotun.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta bayyana shakku dangane da hukuncin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI