Boko Haram: Barnawi na neman goyon baya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Bangaren Kungiyar Boko Haram da Abu Musab Al-Barnawi ke jagoranta na bin salon samun goyon bayan jama’a, ta hanyar nisanta kansu daga hare-hare da ake kai wa yankunan arewa maso gabashi.
Rahotanni sun ce al-Barnawani na yunkurin ganin ya yi mamaya a kauyukan da ke tafkin Chadi tare da kwantar da hankulan mazauna yankin cewa ba za su cutar dasu ba.
Wasu majiyoyi sun ce rikici ya lafa a wasu yankunan arewacin Borno kusa da tafkin Chadi da ke ikon Barnawi da Mamman Nur.
Barnawi dai tsohon mataimaki ne ga shugaban Boko Haram Abubakar shekau kafin su samu sabani kan adawarsa da yadda ake kai wa fararen hula da musulmi hari da sunan da’awar jihadi.
Amma masharhanta da masana harkokin tsaro na ganin cewa Kungiyar Boko Haram da ta shafe shekaru 8 tana kisan mutane a Najeriya na kokarin sake bulo da sabon salon yaki ne.
Dr Muhammad Kabir Isa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria wanda ya dade yana nazari kan rikicin Boko Haram a Najeriya ya ce Barnawi na son tabbatar da cewa kungiyarsa na nan da karfinta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu