Faransa

An shata wa Limamai Ka'idoji a Faransa

Babban Masallacin birnin Paris
Babban Masallacin birnin Paris REUTERS/Christian Hartmann

Babbar Kungiyar addinin musulunci a Faransa (CFCM) ta bayyana amincewa da wani kundin ka’idodi da limaman addinin musuluncin kasar za su yi aiki da shi da nufin dakile tsatstsauran ra’ayi addini da zai tafi daidai da tsarin kasar.

Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da ya rage makwanni a gudanar da zaben shugabancin kasa, a Faransa da ta fuskanci hare haren ta’addanci daga kungiyar IS da ke da’awar jihadi.
Ka’idojin sun kunshi tantance mutum kafin a nada shi Limami.

Batun kafa tsarin ya biyo bayan harin ta’’adanci mafi muni a kasar da aka kai a ranar 13 ga Nuwamban 2015 da ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutane da dama.

Domin tabbatuwar ganin an yi aiki da wannan kundi da aka shirya tsawon lokaci, ana bukatar limaman kasar ta Fransa su yi la’akari da tsarin dokokin jamhuriyar wajen gudanar addinin zaman lafiya, kamar yadda kungiyar limaman ta CFCM, da ta hada manyan kungiyoyin musulmin Faransa ta sanar

An bukaci masalatan Faransa su saka hannu amincewa da wannan kundi, a matsayin wani mataki da zai ba limamin masalacin damar ci gaba da limanci a kasar.

Faransa dai ita ce kasa mai yawan musulmi a Turai kuma akwai Limamai 1,800 yawancinsu daga kasashen Algeria da Morocco da Turkiya da ke bada sallah a masallatai kimanin 2,500.

Sabon tsarin dai ya fara fuskantar dawa daga wasu Malaman Islama da ke bada Sallah a manyan Masallatan Faransa.

Malaman na koken cewa an tsara kundin ka’idojin ne ba tare da tuntubarsu ba.

Babbancin akida tsakanin mabiya addinin na Islama ne dai babban kalubalen aiwatar da tsarin a Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI