Najeriya

Buhari ya tura Jakadun Amurka da MDD

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS

Shugaban Najeriya Muhammadu Muhari ya sanar da tura manyan jakadun kasar da suka kunshi Amurka da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Tarayyar Afrika. Wannan na zuwa bayan sun samu horo kan ayyukansu a fadar shugaban kasa

Talla

Tijjani Bande daga Jihar Kebbi, Buhari ya tura a matsayin jakadan Najeriya a Amurka.

Itegboje Samson daga Jihar Edo ne Buhari ya tura a matsayin sabon jakada a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya a Amurka. Kadiri Audu daga Jihar Kwara aka tura matsayin Jekadan Najeriya a ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Geneva.

Sai Bankole Adeoye a matsayin jekada a Tarayyar Afrika a hedikwatar kungiyar da ke Addis Ababa kasar Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI