CAR

Shugaba Touadera na CAR ya shekara kan mulki

Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra
Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra ISSOUF SANOGO / AFP

A yayin da shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Faustin Archange Touadera ke cika shekara guda akan karagar mulki, al’ummar kasar sun ce, sha’anin tsaro ya inganta amma akwai sauran aiki a gaba.

Talla

Jim kadan da hawansa kan kujerar mulki a bara, Mr. Touadera ya yi alkawarin hada kan kasar wadda ta tsindima cikin rikicin kabilanci tun a shekarar 2013, bayan juyin mulkin da aka yi.

A halin yanzu dai kasar ta fi samun zaman lafiya a karkashin shugaban Touadera amma kashi 60 cikin 100 na kasar na karkashin ikon kungiyoyi masu dauke da makamai.

Al’ummar kasar sun ce, suna ganin alamar farfadowar tattalin arzikin kasar amma akwai sauran aiki a gaba.

Kimanin kashi 48 cikin 100 na jama’ar kasar na fama da yunwa kuma kashi 35 ne kadai ke samun tsaftataccen ruwan sha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI