Afrika

Kasashen Afrika 44 sun soki kasar India bisa gazawa wajen kare dalibansu

Wasu daga cikin shugabannin kasashen nahiyar Afrika da suka yi tur da gazawar kasar India wajen kawo karshen cin zarafin dalibai daga nahiyar Afrika da wasu 'yan kasar ke yi.
Wasu daga cikin shugabannin kasashen nahiyar Afrika da suka yi tur da gazawar kasar India wajen kawo karshen cin zarafin dalibai daga nahiyar Afrika da wasu 'yan kasar ke yi. dailystar.com.lb

Jakadun kasashen Afirka 44, sun soki gwamnatin kasar India, kan yadda ta kasa daukar matakan kare lafiyar dalibai ‘yan Afirka wadanda ake ci gaba da kai musu hari a kasar.

Talla

Wata sanarwar da Jakadun suka bayar, ta nuna yadda gwamnatin India ta kasa daukar matakan da suka dace don kawo karshen matsalar da ke kara yawaita.

Jakadun sun bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin, wanda suka bayyana shi a matsayin wariyar launin fata.

An dai kwashe kawanaki ana kai hare hare kan daliban, akasarin su yan Najeriya ba tare da daukar wani mataki ba.

A shekara ta 2013, wasu gungun indiyawa suka yi wa wani dan Najeriya kisan gilla a garin Goa, inda aka rawaito wasu daga cikin ‘yan siyasar kasar na bayyana ‘yan Najeriya a matsayin cutar Sankara.

A shekara ta 2014 kuma an zargi ministan shari’ar da cin zarafin wasu mata daga nahiyar Afrika, bisa zarginsu da cewa mata ne masu zaman kansu.

A halin da ake ciki ‘yan sandan India, sun kame mutane 6 daga cikin 10 da ake zargi da kai hari kan dalibai ‘yan Afrika a satin da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.