Isa ga babban shafi
Libya

Bakin haure 100 sun bace a gaban tekun Libya

Jamian kula da gaban teku na Libya a lokacin da suke taimakawa wasu bakin haure da jirginsu ya kife a teku.
Jamian kula da gaban teku na Libya a lokacin da suke taimakawa wasu bakin haure da jirginsu ya kife a teku.
Zubin rubutu: Garba Aliyu
Minti 1

Jami'an tsaron gaban tekun kasar Libya sun sanar da bacewar wasu bakin haure akalla 100 bayan da kwale-kwalensu ya kife a lokacin da suka bar gaban tekun Libya kusa da birnin Tripoli.

Talla

Mai Magana da yawun jami'an gaban tekun Ayoub Qassem ya bayyana cewa 23 daga cikin bakin hauren an sami kubutar dasu daga kwale-kwalen dake dauke da mutane 120.

A cewar sa kwale-kwalen kifewa yayi a lokacinda ya tashi daga gaban ruwan na Libya.

Gaban tekun kasar Libya ta kasance mashigin farko da bakin haure ke bi daga nahiyar Africa domin tafiya Turai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.