Afrika ta Kudu

An yi zanga-zangar kyamar Zuma a Afrika ta kudu

An yi kyamar zanga-zangar kyamar shugaba Zuma a Pretoria
An yi kyamar zanga-zangar kyamar shugaba Zuma a Pretoria REUTERS/ James Oatway

Jam’iyyu da kungiyoyin adawa sun gudanar da gagarumar zanga-zanga a Afrika ta kudu domin neman shugaba Jacob Zuma ya sauka daga mulkin kasar.

Talla

Babban gangamin da aka yi a birin Pretoria da ya sami halarcin dubban jama’a, inda suka yi jerin gwano zuwa ofishin Shugaban kasar a dai dai wani lokaci da Shugaban ke bukin cika shekaru 75 da haihuwa.

Sauke Ministan kudi na kasar Pravin Gordhan wanda ake ganin yana da kima a idanun jama’a na daga cikin manyan abubuwan da ya harzuka mutanen kasar, da batun zargin yawaitan cin hanci da rashawa da kuma batun rashin ayyukan yi da jinkirin farfadowar tattalin arzikin kasar.

A zanga-zangar da ya hada kawunan Kungiyoyin Economic Freedom Fighters EFF da Jamiyyar Democratic Alliance DA da dai wasu kananan jamiyyu da basa ko ga maciji a baya yanzu sun hade albarkacin adawa domin nuna kyamar Gwamnatin Jacob Zuma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.