Nijar

An cafke 'yan sanda 3 bisa zargin dukar dalibai

'Yan sanda da masu zanga-zanga a Nijar
'Yan sanda da masu zanga-zanga a Nijar Boureima Hama-AFP

Rundunar ‘yan sandan Jamhuriyar Nijar ta kama jami’anta uku wadanda ake zargi da gallaza wa dalibai azaba ta hanyar duka a lokacin tarzomar da aka yi a birnin Yamai ranar litinin ta makon jiya.

Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandar Adily Toro, ya ce za a hukunta, sakamakon wani hoton bidiyo ya nuna yadda suke dukar wani dalibi, sannan kuma suna umurtar sa da ya rera taken da ke jinjina wa ‘yan sanda.

Tarzomar ta makon jiya ta tsananta, inda aka samu asarar rayuwar dalibi daya tare da raunata wasu masu tarin yawa.

A yunkurin kwantar da hankula, a ranar lahadin da ta gabata an gana tsakanin shugaban kasar Issifou Mahamadou da wakilan dalibai, kafin daga bisani a yi irin wannan ganawa tsakanin Firaminista Birji Raffini da wakilan dalibai, iyayan dalibai, kungiyoyin kare hakkin bil’ama da kuma shugabannin addinai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.