Bakonmu a Yau

Farfesa Dandago kan bunkasar arzikin kasashen Afrika

Sauti 03:14
Shugaban IMF Christine Lagarde tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja
Shugaban IMF Christine Lagarde tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja

Hukumar bada lamuni ta duniya IMF ta yi hasashen cewa za a samu bunkasar attalin ariziki a kasashen kudu da sahara da kusan kashi uku a bana sakamakon farfadowar tattalin arzikin manyan kasashen yankin kamar Najeriya da Afrika ta kudu da kuma Angola. Hasashen na IMF ya bayyana cewa, Najeriya za ta samu habakar tattalin arziki da kusan kashi daya a 2017 bayan ya tabarbare a 2016 sakamkon faduwar farashin danyen mai da kuma matsalar tsagerun Neja Delta. Awwal Janyau ya tattauna da Farfesa Kabiru Isah Dandago, Kwamishin kudi na Jihar Kano.