DR Congo

Za a dawo da gawar Tshisekedi Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo

Akwatin dake dauke da gawar Etienne Tshisekedi
Akwatin dake dauke da gawar Etienne Tshisekedi REUTERS/Francois Lenoir

A Jamhuriyar Demokradiyyar Congo iyalan Jagoran dan adawa marigayi Etienne Tshisekedi sun sanar da ranar da za a dawo da gawar mammacin a wannan kasa.

Talla

Tshisekedi Shugaban jam’iyyar UDPS ya rasu ne ranar 1 ga watan fabrairu shekarar 2017,wanda bayan rasuwar sa ake ci gaba da rikici tsakanin magoya bayan jam’iyyar sa, iyalan sa da gwamnati dangane da wurin da ya dace a bine shi.

Sanarawa daga iyalan mammacin na tabbatar da cewa ranar 12 ga watan Mayu ne gawar Etienne Tshisekedi za ta dawo Jamhuriyar demokradiyyar Congo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.