Kamaru

Kamaru ta daure wakilin RFI Hausa Ahmed Abba shekaru 10

RFI ta yi allawadai da hukuncin da Kamaru ya yanke wa Ahmed Abba, wakilin sashen Hausa
RFI ta yi allawadai da hukuncin da Kamaru ya yanke wa Ahmed Abba, wakilin sashen Hausa facebook

Kotun sojin Kamaru a Yaounde ta zartar da hukuncin daurin shekaru 10 a yau Talata akan Ahmed Abba, kan alaka da ayyukan ta’addanci, laifin da babu hujjoji akan dan jaridar da ke aiko wa sashen hausa na RFI da rahotanni daga yankin arewa mai nisa.

Talla

Bayan daurin shekaru 10, kotun kuma ta ci Abba tarar kimanin yuro 85,000.

Amma Lauyan da ke kare shi ya ce za su daukaka kara saboda babu wasu hujjoji da ke tabbatar da Ahmed Abba ya aikata laifin da aka ce an same shi da aikatawa.

Shari’ar da ta dauki dogon lokaci ana yi ya janyo hankalin kasashen duniya da kungiyoyin kare Yan Jaridu, musamman Reporters Without Borders.

Abba ya shafe kusan shekaru biyu a tsare cikin yanayi na wahala da azabtarwa tun watan Yulin 2015 da aka kama shi a yankin arewa mai nisa.

Hukumomin RFI sun dade suna allawadai da kama ma'aikacin na sashen hausa ba tare da Kamaru ta gabatar da hujjojin dalilin tsare shi ba.

Kungiyoyin kare hakkin 'Yan Jaridu sun yi watsi da hukuncin inda suka bukaci gaggauta sakin dan Jaridar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.