Kamaru

Ahmed Abba: Faransa ta yi allawadai da hukuncin kotun Kamaru

Idan Ahmed Abba bai biya kudin tara ba za a kara masa hukuncin daurin shekaru 5
Idan Ahmed Abba bai biya kudin tara ba za a kara masa hukuncin daurin shekaru 5 facebook

Gwamnatin Faransa ta bayyana damuwarta a hukumance dangane da hukuncin dauri na shekaru 10 tare da biyan tarar CFA milyan 55 da kotun Kamaru ta yanke wa Ahmed Abba wakilin Sashen Hausa na RFI a jiya Litinin.

Talla

Sanarwar da kakakin ma’aikatar wajen Faransa Romain Nadal ya fitar a yau talata, ya bayyana hukuncin a matsayin abin damuwa, yana mai mai fatan karar da lauyoyin Abba suka daukaka yi zai kai ga samar wa dan jaridar ‘yancinsa a cikin gaggawa.

Abba da ke aiko wa sashen hausa na RFI da rahotanni daga yankin arewa mai nisa mai fama da rikicin Boko Haram an yanke masa hukuncin ne kan laifin taimakawa ta’addanci.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da na kare ‘yan jaridu dukkaninsu sun yi allawadai da hukuncin.

Abba ya shafe kusan shekaru biyu a tsare cikin yanayi na wahala da azabtarwa tun watan Yulin 2015 da aka kama shi a yankin arewa mai nisa.

Hukumomin RFI sun dade suna allawadai da kama ma'aikacin na sashen hausa ba tare da Kamaru ta gabatar da hujjojin dalilin tsare shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.