Najeriya

Fargaba dangane da lafiyar shugaba Muhammadu Buhari

Muhammadu Buhari, shugaban tarayyar Najeriya
Muhammadu Buhari, shugaban tarayyar Najeriya REUTERS

Ana ci gaba da nuna fargaba dangane da lafiyar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, sakamakon yadda shugaban ya kaurace wa zaman majalisar ministocin kasar da aka gudanar a jiya laraba.

Talla

An dai gudanar da taron majalisar ministocin na jiya ne karkashin jagorancin mataimakin shugaban Yemi Osinbajo, a daidai lokacin da ‘yan kasar ke nuna fargaba dangane da raguwar fitowar shugaban baina jama’a kamar yadda aka saba gani a baya.

Tun bayan dawowarsa daga jinya a kasar Ingila a ranar 10 ga watan maris da ya gabata, shugaban Muhammadu Buhari ya rage fitowa bainar jama’a ko kuma halartar taruka.

To sai dai, mai taimaka wa shugaban kan harakokin sadarwa Malam Garba shehu ya ce bai kamata jama’a su tayar da hankulansu ba domin kuwa shugaban na cikin koshin lafiya a cewarsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.