Jamus-Libya

Jamus ta soki kafa sansanin ‘yan gudun hijira a Libya

Bakin haure basu dai na tururuwa Turai ba
Bakin haure basu dai na tururuwa Turai ba Abdullah ELGAMOUDI / AFP

Ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel ya ce kasar sa ba za ta goyi bayan kafa sansanin ‘yan gudun hijira a kasar Libya ba, a matsayin hanyar dakile kwararar baki zuwa Turai.

Talla

Kalaman na shin a nuna shirin watsi da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Italiya da Gwamnatin Libya da ke samun goyan bayan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Turai wanda ke nuna shirin bada kudi dan kafa sansanin.

Daga cikin baki 500,000 da suka isa Italiya a cikin shekatu 3 da suka gabata, akasarin su sun bi ne ta cikin kasar Libya.

A ganawar da suka yi da ministan harkokin wajen Libya Faki Mahamat, Gabriel ya ce ya zama wajibi a lalubo wata hanya ta dabam domin magance matsalar.

Jamus ta yi tayin bai wa Libya agajin euro miliyan 27 dan hana baki bi ta kasar ta zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.