Afrika ta Kudu

An saki mutumin da ke son kashe shugaban Afrika ta Kudu

Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma a Majalisar Dokokin kasar
Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma a Majalisar Dokokin kasar REUTERS/Sumaya Hisham

Wata Kotun Afrika ta Kudu ta bada belin wani mutum da ake zargin sa da kitsa kashe manyan 'yan siyasar kasar, cikinsu har da shugaba Jacob Zuma don ganin an samu sauyin gwamnati.

Talla

Rahotanni sun ce mutumin mai suna Elvis Ramosebudi mai shekaru 33, ya tuntubi wasu kamfanoni masu zaman kansu don samun kudaden da zai yi amfani da su wajen aiwatar da kisan.

Wanda ake zargin ya lissafa mutane 19 a matsayin wadanda zai hallaka da suka hada da wadanda ake zargin sun amfana da kudaden cin hanci tare da iyalan gidan Gupta masu karfin fada aji a gwamnatin shugaba Zuma.

Alkalin kotun ya bada belin matashin akan kudin da ya kai Dala 222.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.