Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo

Jamhuriyar Congo: Wadanda suka kamu da cutar Ebola sun karu

Mutane biyu sun sake kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Congo.
Mutane biyu sun sake kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Congo. appsforpcdaily.com

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce an sake gano karin mutane biyu da suka kamu cutar Ebola, a Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo, kwana guda bayanda hukumar ta yi shelar sake bullar cutar a kasar.

Talla

Zuwa yanzu dai hukumar ta WHO ta ce an gano jimillar mutane 11 kenan da suka harbu da annobar, ciki har da mutane 3 da suka mutu bayan kamuwarsu da cutar, a garin Likati da ke lardin Bas Uele a arewacin kasar ta jamhuriyar Congo.

Jami’an lafiya sun ce mutum na farko ya kamu da cutar Ebolan ce, a ranar 22 ga watan Afrilun da ya gabata.

Sau bakwai Janmhuriyar Congo ta yi fama da barkewar annobar cutar a baya, kuma na karshe shi ne wanda ya auku a shekara ta 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.