Nijar-Libya-Turai

Za a samar da rundunar dakile kwararar bakin dake zuwa Turai

Wasu daga cikn bakin haure dake kokarin tsallakawa
Wasu daga cikn bakin haure dake kokarin tsallakawa

Ministocin cikin gidan kasashen Jamus da Italia sun bukaci kafa wata rundunar kungiyar kasashen Turai tsakanin kasashen Libya da Nijar dan dakile kwararan bakin dake tafiya Turai.

Talla

A wata wasikar hadin gwuiwa da ministocin biyu Thomas de Maiziere da Marco Minniti suka aikewa Kungiyar, sun bayyana dalilin kara daukar kwararan matakai dan dakile yadda dubban baki ke jefa kan su cikin haddura wajen bi ta cikin teku domin tsallakawa Turai.

Kasar Italia ta ce tsakanin watan Maris zuwa Afrilu ta karbi bakin da suka kai 42,500.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.