Africa ta Kudu

An Sace Sarkin Kauyen da Nelson Mandela ya fito a kasar Africa ta Kudu.

Marigayi Nelson Mandela
Marigayi Nelson Mandela RFI

Wasu ‘yan bindiga sun sace wani basaraken kauyen da Marigayi Nelson Mandela na Africa ta Kudu ya fito na Mtata dake gabashin gunduman Cape, kamar yadda ‘yan sanda suka sanar.

Talla

Yarima Mankunku Dalindyebo wanda aka sace  ya kasance shine dan uwan Sarki Buyelekhaya Dalindyebo wanda yake zama gidan yari na tsawon shekaru 12 tun watan Disamba na 2015 saboda zargin haddasa gobara, da sace mutane.

‘Yan sanda sun bayyana cewa an sace shi ne a garin na Mtata, kuma suna ci gaba da binciken lamarin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.