RFI

RFI Hausa ta shiga zukatan al’umma cikin kankanin lokaci- Azare

RFI Hausa @10 celebration in Lagos
RFI Hausa @10 celebration in Lagos RFIHAUSA/Awwal

RFI Hausa da aka kaddamar a ranar 21 ga watan Mayun 2007 ta cika shekaru 10 da fara watsa shirye-shirye, wanda shi ne sashe na farko da RFI ta bude a Afrika kafin Swahili da Mandingo.

Talla

Lokacin da aka bude sashen Hausa na RFI ba a taba tunanin zai iya gogayya da manyan kafofin yada labarai na waje ba da suka jima suna watsa shirye shiryensa a harshen hausa.

An dai gudanar da bikin ne a birnin Lagos na Najeriya tare da halartar masu saurare da manyan baki daga ciki da kuma wajen kasar, da suka hada da jekadan Faransa a Najeriya da Hon Abdurrazak Namdas wanda ya wakilce kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara da Sarakunan gargajiya.

Farfesa Yakubu Azare na sashen koyar da harsunan Najeriya a Jami'ar Bayero shi ya wakilci Farfesa Umar Fate a matsayin babban mako mai jawabi a bikin.

A cikin jawabinsa, Farfesa Azare ya yaba da sashen hausa na RFI ke gabatar da ayyukansa wajen yada labarai ba tare da nuna fifiko ba tare da tsage gaskiya da wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

“Cikin Kankanin lokaci RFI Hausa ta samu nasarar shiga zukatan al’umma” a cewar Farfesa Azare.

Farfesa ya kara da cewa a yanzu ba za a iya ambatar sauran manyan kafafen yada labarai na kasashen waje ba tare da RFI Hausa ta kasance a sahun gaba ba.

Cikin shekaru 10 RFI Hausa na da yawan masu saurare sama da miliyan shida a kasashen yammacin Afrika da sauran sassan duniya.

A Najeriya, kimanin mutane miliyan uku ke sauraren RFI a kowace rana, bayan dimbin masu saurare a Nijar da Kamaru da Chadi da Ghana da kasashen Sudan da Burkina Faso da Mali da kuma Senegal.

Shafin Intanet na RFI Hausa na samun maziyarta sama da miliyan daya a wata, kashi 80 daga cikinsu daga Najeriya.

RFI Hausa ta yi amfani da bikin cika shekaru 10 domin yin kira ga mahukuntan Kamaru su gaggauta sakin wakilinta a kasar Ahmed Abba wanda aka zartarwa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.