DR Congo

Ebola ta sake kisa a Congo

WHO ta sanar da sake bullar Ebola a Congo
WHO ta sanar da sake bullar Ebola a Congo appsforpcdaily.com

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce wani mutum da ake zaton ya kamu da cutar Ebola ya mutu a kauyen Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, abinda ya kawo mutane 4 da suka mutu daga cikin 37 da suka kamu da cutar.

Talla

Eugene Kabambi, mai Magana da yawun hukumar, ya ce daga cikin mutne 37, 2 kawai aka tabbatar da cewar Ebola ce ta hallaka su, kana ana ci gaba da gudanar da bincike kan 32.

Kabambi ya ce yanzu haka mutane 416 da suka yi mu’amala da wadanda ake zaton sun kamu da cutar ake sa ido akan su, ko da za’a iya ganin wata shaida da ke nuna alamar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.