Sudan

Al-Bashir ya zargi Masar da goyon bayan ‘yan tawayen kasar

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir Ashraf Shazly/AFP Photo

Shugaban kasar Sudan, Omar al-Bashir, ya zargi gwamnatin Masar da goyon bayan kungiyoyin ‘yan tawayen da ke tada kayar baya a yankin Darfur.

Talla

Al- Bashir ya furta zargin ne, yayinda ya rage kwanaki, ministan harkokin wajensa, Ibrahim Ghandour, ya ziyarci Masar a ranar 31 ga watan Mayu, don tattauna kawo karshen tsamin dangantakar kasashen biyu.

Cikin watannin da suka gabata dangantaka ta yi tsami sosai tsakanin Sudan da Masar, hakan kuma ya samo asalli ne a dalilin takaddamar da suke yi kan wasu ka’idojin huldar kasuwanci musamman a kudancin kasar ta Masar.

Akwai kuma batun saukaka ka’idojin samun takardun izinin shiga kasa da ga kowane bangare, takaddamar da ke barazanar rusa alaka ko yarjejeniyar cinikayya da ke tsakanin kasashen biyu.

Cikin jawabin da ya gabatar gaban manyan jami’an sojin kasar, shugaba al-Bashir ya ce bada dadewa bane sojin kasar suka kwace tankokin yakin kasar Masar daga hannun mayakan ‘yan tawaye da ake gwabzawa da su a kudancin yankin Darfur da ke fama da rikici.

Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Masar ta musanta zargin, marawa ‘yan tawayen baya, wajen tada zaune tsaye.

An dai kwashe tsawon lokaci sojin Sudan na gwabza fada da kungiyoyin ‘yan tawaye a wasu yankuna da ke kudancin kasar Sudan.

A farkon wannan shekarar ce gwamnatin Amurka, ta ce a shirye take ta dagewa kasar takunkumin karya tattalain arzikin da ta dade da kakaba mata, amma da shardin tilas ta dawo da zaman lafiya a yankin Darfur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.