Birtaniya-Libya

'Yan sandan Libya sun cafke mahaifin maharin Manchester

'Yansanda su tsaurara matakan tsaro a birnin Manchester
'Yansanda su tsaurara matakan tsaro a birnin Manchester REUTERS/Stefan Wermuth

'Yan Sanda a kasar Libya sun kama mahaifin matashin da ake zargi da kai harin Manchester wanda ya kashe mutane 22 tare da wan sa a Tripoli.

Talla

Wannan na daga cikin matakan da ake dauka dangane da binciken wadanda ake zargin suna da hannu a harin.

Rundunar yaki da ta’addanci da ke Libya ta sanar da kama Ramadan Abedi, mahaifin Salman Abedi da ake zargi da kai harin, tare da wan sa Hashem Abedi a unguwar Ayn Zara da ke Tripoli.

Rundunar da ake kira rada, ta ce tana rike da Hashem ne saboda zargin cewar ya yi ta tattaunawa da Salman kuma ana kyauatata zaton shi ma yana shirin kai hari a cikin Libya.

Kakakin rundunar tsaron Ahmed Bin Salem ya ce suna da shaidar da ke nuna musu cewar matasan biyu na da alaka da kungiyar ISIS, saboda sun kwashe sama da wata guda da rabi sun bin diddigin su.

Jami’in ya ce kanin na sa ya bar London zuwa Tripoli ranar 16 ga watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.