Mali

'Yan bindiga sun kona makarantar boko a Mali

Dakarun MDD Minusma na sintiri a Mali
Dakarun MDD Minusma na sintiri a Mali SEBASTIEN RIEUSSEC / AFP

Wasu da ake zargin cewa masu da'awar jihadi ne sun kona wata makarantar boko a garin Ndojiga da ke tsakiyar kasar Mali, karo na farko da aka kai irin wannan hari daga lokacin kasar ta samin kanta a hannun 'yan ta'adda.

Talla

Shaidu sun ce maharan sun cinna wa makarantar wuta bayan da suka yi harbi a iska domin tarwatsa jama'a, tare da furta barazanar cewa za su kai irin wannan hari kan wasu makarantun kasar.

Har ila yau 'yan bindigar sun yi wa wasu mutane biyu duka a makarantar. Rundunar jami'an tsaro ta Jandarma a garin Mopti wanda shi ne shalkwatar lardin da lamarin ya faru sun tabbatar da cewa lalle an kai harin.

Duk da cewa Mali ta share tsawon shekaru 4 tana fama da kungiyoyin da ke da'awar jihadi da suka hada da Ansaruddin da kuma Mujoa, wannan ne karo na farko da aka kona makarantar boko a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI