Masar

Sojin Masar sun kai farmaki a gabashin kasar Libya

Motar da ke dauke da mabiya addinin Krista, da 'yan bindiga suka budewa wuta a birnin Cairo na Masar.
Motar da ke dauke da mabiya addinin Krista, da 'yan bindiga suka budewa wuta a birnin Cairo na Masar. TV Grab / Nile News / AFP

Sojin saman Masar, sun kai farmaki kan wasu sansanoni a kasar Libya, da suke zargi da, horar da mayakan ‘yan ta’adda da suka hallaka wasu mabiya addinin Kirista 29 da kuma raunata wasu 24 a ranar Juma’ar da ta gabata.

Talla

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce, sojin Masar din sun kai farmakin ne har sau shida, kan wasu sansanoni ne dake yankin Derna, a gabashin kasar ta Libya.

Tawagar mabiya addinin Kiristan dai na kan hanyarsu ce ta zuwa wurin ibada, a lokacin da ‘yan bindigar suka bude musu wuta, a Minya da ke tsakiyar birnin Cairo.

A sanarwar da ta fitar, itama rundunar sojin Libya ta tabbatar ta sanar da goyon bayan farmakin da sojin Masar din suka kaddamar kan 'yan ta'addan, inda ta ce itama tabada tata gudunmawar wajen kai farmakin.

Wani mazaunin yankin na Derna ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun jiwo karar fashewar bama-bamai har sau hudu, a sansanin mayakan kungiyar Majlis al Shura da ke tada kayar baya.

Sai dai cikin wani faifan bidiyo da suka fitar, kakakin mayakan Mohamed al-Mansouri ya ce farmakin na sojin saman Masar bai illata ko da bangare guda ba na sansanoninsu, sai dai gidajen fararen hula.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.