Libya

Bakin-haure dubu 10 aka ceto a tekun Libya

Bakin haure na ci gaba da mutuwa a Teku
Bakin haure na ci gaba da mutuwa a Teku © P Bar/SOS Méditerranée

Bakin-haure kusan dubu 10 aka ceto a tekun Libya cikin kwananki 4 da suka gabata, cikinsu mutane 54 sun kwanta dama.

Talla

A cewar hukumomin Libyan da Italiya, a jiya Assabar Sojoji, sun ceto mutane 126 da suka fito daga yankunan Sahara domin isa Italiya cikin kanana jiragen.

Kana a ranar Juma’a mutane 1,200 aka ceto a Libya, bayan 2,200 da aka gano cikin kanana jiragen ‘yan kasuwa.

Batun mutuwar Bakin-haure a hanyarsu ta isa Turai na ci gaba da ciwa mahukunta tuwo a kwarya la'akari da cewa matakan da ake dauka sun gaggara gamsuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.