Libya

Masar ta sake kai hari kan IS a Libya

Masar ta kaddamar da yaki akan Mayakan IS a Libya
Masar ta kaddamar da yaki akan Mayakan IS a Libya REUTERS/Stringer

Masar ta kaddamar da sabbin hare-haren sama kan sansanonin ‘yan tawaye da ke Libya bayan ta zarge su da hannu a harin da ya hallaka Kiristoci kusan 30 a karshen makon jiya.

Talla

Shugaban Masar Abdul Fatah Al Sisi ya bayyana cewa, shi ne ya bada umarnin kai farmakin kan sansanonin ‘yan tawayen a Libya, yana mai cewa, a can ne aka ba Maharan horo.

Al-Sisi ya ce, Masar ba za ta yi kasa a gwuiwa ba wajen ci gaba da ragargazan ‘yan tawayen a ciki da wajen kasar.

Majiyoyin sojin Masar sun tabbatar cewa, ko a karshen makon jiya, sai da jiragen yakin kasar suka yi lugudan wuta a yankin Derna, in da Kungiyar IS ta fara kafa kwacewa a 2014 a Libya.

Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta ce, ta aika wasika ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kan hare-haren da kasar ke kai wa a Libya musamman don kare kanta daga barazanar ‘yan ta’adda

Wannan dai na zuwa ne bayan wasu ‘yan bindiga rufe da fuskokinsu sun kai hari kan motar wasu mabiya addinin Kirista a lardin Minya, in da suka hallaka 29 daga cikinsu tare da jikkata 24.

Harin na baya-bayan nan na zuwa ne wata guda da aka kai wa wasu majami’u biyu a Masar harin bam, in da mutane 45 suka mutu, Kuma IS ta fito ta dauki alhakin harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.