Africa ta Kudu

Zuma ya tsallake rijiya da baya a taron ANC

Zanga-zangar kyamar shugaba Zuma a Johannesburg
Zanga-zangar kyamar shugaba Zuma a Johannesburg REUTERS/Mike Hutchings/File Photo

Shugaban kasar Africa ta Kudu Jacob Zuma ya tsallake rijiya da baya wajen babban taron Jam’iyar da ke mulkin kasar inda aka so jefa kuri’ar rashin amincewa da shi.

Talla

Taron jam’iyar da ke mulki ANC da aka fara jiya lahadi, za a kwashe kwanaki uku ana yi a birnin Pretoria.

Wasu ‘Ya‘yan jam’iyyar sun bukaci shugaban kasar ne da ya sauka tun bayan matakin koran Ministan kudi na kasar Pravin Gordhan wanda ake kallon yana da kima a idanun jama’a.

Majiyoyi daga dakin taron na cewa an yi ta yunkurin tsige shugaban kasar a taron da aka fara amma kuma Shugaban Jam’iyyar ya yi uwa ya yi makarbiya wajen hana daukan matakin.

Sakataren Jamiyyar ta ANC Gwede Mantashe ya shaidawa manema labarai a wajen taron cewa taron ya yi armashi ganin babu wani mummunan abinda ya faru.

A na saran Jami’yyar ta ANC ta zabi wanda zai maye gulbin shugaba Jacob Zuma a watan 12 da ke tafe, kafin babban zaben kasar na shekara ta 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.