Libya

MDD ta kaddamar da gidauniyar taimakawa Libya

Tattaunawar kubutar da Libya daga kunci
Tattaunawar kubutar da Libya daga kunci KHALED DESOUKI / AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar Dala miliyan 75 dan shawo kan matsalar 'yan gudun hijira da yanzu haka ta addabi kasar Libya.

Talla

Kwamishinan kula da ‘Yan gudun hijira Filippo Grandi ya ce za’ayi amfani da kudin wajen tallafawa bakin da suka tagayyara a kasar ta Libya.

Majalisar ta ce yanzu haka daruruwan baki ne suka makale a kasar a kan hanyar su ta zuwa Turai, kuma wasu daga cikin su ana tsare da su a gidan yari.

Kungiyar da ke kula da kwararar bakin ta ce akalla baki 1.481 suka mutu a teku a cikin watanni 5 da suka gabata, yayin da wasu 1,720 suka bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.