Habasha

An toshe Intanet saboda satar jarabawa a Habasha

Dalibai a Habasha na satar jarabawa ta hanyar Intanet
Dalibai a Habasha na satar jarabawa ta hanyar Intanet REUTERS/Kacper Pempel/Files

Kasar Habasha ta toshe Intanet a fadin kasar domin dakile yunkurin satar jarabawar kammala sakandare da dalibai ke yi a kafofin sadarwa na intanet. Matakin ya durkusar da ‘yan kasuwa da ke dogaro da intanet a kasar.

Talla

Tun a ranar 31 ga Mayu da aka soma jarabawar, hukumomin Habasha suka toshe intanet domin hana satar jarabawar.

Dalibai dai na amfani da kafofin sadarwa na intanet domin raba takardar tambayoyin jarabawar da aka sato.

Gwamnatin Habasha ta ce ta dauki matakin ne domin kaucewa yadda dalibai suka yi satar jarabawar a bara ta hanyar musayar tambayoyin jarabwar a kafofin sadarwa na intanet kamar Facebook da Twitter da Whatsapp.

Intanet din zai ci gaba da zama a toshe a fadin kasar har zuwa kammala jawabawar a ranar 8 ga wata nan na Yuni.

Matakin dai ya shafi ofisoshin gwamnati da kuma ‘yan kasuwa da ke cin abinci da intanet.

Gwamnatin Habsha ta taba toshe intanet a bara na tsawon makwanni sakamakon zanga-zangar kin jin gwamnati da har ta kai aka kafa dokar ta-baci a watan Oktoban bara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.