Africa ta Kudu

Shugaban Africa ta Kudu Zuma ya Musanta Mallakan Gida a Dubai

Shugaban Africa ta Kudu  Jacob Zuma
Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma REUTERS/Rogan Ward

Shugaban kasar Africa ta Kudu Jacob Zuma ya musanta zargin da ake yi masa a kasar cewa ya mallaki wani katafaren gida a Dubai na Daular Larabawa.

Talla

Kafofin watsa labarai dake kasar suka fara baza cewa wani danginsa ya saya masa katafaren gida a Dubai.

Ire-iren wadannan zarge-zarge da dama ne aka bankado makon jiya, bayan ya tsallake siratsin jefa masa kuri'ar rashin amincewa dashi a taron jam'iyyar ta su ta ANC.

Jaridar Sunday Times da ake buga ta a kasar ta ce ta na da hujjoji da suka tabbatar mata cewa Iyalan Gupta ‘yan kasar India dake zaune a Africa ta Kudu suka sayawa Jacob Zuma gida na kasaita a Dubai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.