Ruwan sama da iska ya lalata runfunan ‘yan gudun hijira a Borno
Wallafawa ranar:
Ruwan sama da aka tafka mai tafe iska ya lalata rumfunan ‘yan gudun hijira sama da 1,000 a sansanonin da suke rayuwa a Jihar Borno, wanda ya shafi mutane kusan 5,000.
Wannan ya kara fito da girman matsalar da ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram ke fuskanta na rashin matsuguni mai kyau da inganci a Jihar Borno.
Rahotanni sun ce an shafe tsawon sa’o'i uku ana maka ruwan saman da iska wanda ya lalata runfunan na ‘yan gudun hijira a Maiduguri da Kaga da Konduga.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan halin da ‘yan hudun hijira za su shiga a Najeriya musamman watanni uku zuwa hudu da za a shafe ana ruwan sama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu