Afrika

Ilimin mata ya habbaka a nahiyar Afrika

Wasu dalibai mata da ke karatu a wani aji na wucin gadi da ke sansanin 'yan gudun hijirana Abu Shouk a yankin Darfur
Wasu dalibai mata da ke karatu a wani aji na wucin gadi da ke sansanin 'yan gudun hijirana Abu Shouk a yankin Darfur

Wani rahotan hadin kai tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Raya Kasashen Afrika da kuma Kungiyar Tattalin Arziki da ci gaba ya ce, an samu karuwar yara mata da ke kamamla karatun sakandare a nahiyar Afrika da kuma karuwar kudaden da ake kashewa wajen kula da su. 

Talla

Sai dai rahotan ya ce duk da wannan ci gaban, har yanzu akwai yaran da ake tilasta wa auren wuri da kuma aikin karfi .

Rahotan binciken da aka wallafa a makon jiya ya ce kashi biyu bisa uku na 'yan matan da ke Afrika ta Gabas da kashi uku bisa hudu da ke Afrika ta Tsakiya sun kammala karatun sakandare tsakanin shekarar 2014 zuwa 2015.

Masanan da suka gudanar da binciken sun bukaci kara damara don ganin an taimaka wa wadancan marasa karfin da ake tilastawa auren wuri ko kuma aiki saboda talauci don ganin cewa su ma sun samu ilimin da ya dace domin ganin an cimma muradun karnin da aka shirya a shekarar 2030.

Paolo Babos, jami’in hukumar UNICEF ya ce, akasarin 'yan matan da ba su da damar karatu sun fito ne daga gidajen matalauta, abin da ke mu su wahalar zarcewa sakandare bayan kammala karatun firamare.

Sai dai ya yaba da sabon tsarin da aka samu a fadin Afrika na bai wa 'yara matan ilimin da ya dace domin ganin an dama da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.