Mali

An kashe Dakarun Majalisar Dinkin Duniya uku a arewacin Mali

Mayaka yankin Kidal na arewacin Mali
Mayaka yankin Kidal na arewacin Mali AFP/SOULEYMANE AG ANARA

An kashe dakarun MDD uku tare da raunata wasu akalla takwas a yankin Kidal da ke arewacin Mali a wannan juma’a.   

Talla

Sanarwar da rundunar ta Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA ta fitar ta bayyana cewa an kai wa dakarun hari ne da makamai masu linzame a daidai lokacin da suke kan aikin tallafa wa dakarun Mali domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Ana samun karuwar hare-hare akan dakarun na MDD da ma na kasar ta Mali a yankin Kidal da ke kallo a matsayin babbar cibiyar Azibinawa ‘yan tawaye da kuma sauran kungiyoyin da ke dauke da makamai a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.