Wasanni

Super Eagles za ta karbi bakuncin Bafana Bafana ranar asabar

Nigeria-super Eagles
Nigeria-super Eagles

Gobe asabar za a buga wasanni da dama domin samun tikitin shiga gasar neman kofin kwallon kafa na Afirka.

Talla

Daya daga cikin manyan wasannin da za a yi a gobe shi ne fafatawar Najeriya da Afrika ta Kudu a garin Uyo da tarayyar Najeriya.

Akwai dalilai da dama da suka ana kallon wannan wasa na gobe da muhimmanci:

Da farko dai shi ne yadda Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu ta zame wa Super Eagles kadangaren bakin tulu har ma ta hana Najeriya zuwa gasar neman kofin Afirka da aka yi Equatorial Guinea a shekara ta 2015, kuma tun a wannan lokaci ne Najeriya ta gaza doke Afirka ta duk a lokacin da suka hadu a filin wasa.

Tun a ranar larabar da ta gabata ne ‘yan wasa na Afirka ta Kudu suka isa Najeriya, kuma sun zo ne a matsayin tawaga mai kunshe da ‘yan wasa, masu horas da su da kuma jami’an kiwon lafiyarsu a jimilce mutane 35.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.