Isa ga babban shafi
Gabon

Hukumomin Gabon Sun Kori Ma'aikaciya Saboda Tuntuben Harshe

Shugaban Gabon Ali Bongo
Shugaban Gabon Ali Bongo ZACHARIAS ABUBEKER / AFP
Zubin rubutu: Garba Aliyu
1 min

Hukumomi a kasar Gabon sun yi wa wata mai karanta labarai a tashan gidan Talabijin na kasar kokar kare daga aikin saboda tuntuben harshe a lokacin karanta labarai inda ta furta cewa  Shugaban kasar Ali Bongo ya mutu.

Talla

Dazun nan aka sanar da Koran ma'aikaciyar Wivien Ovandong saboda mummunar kuskure da ta aikata shekaranjiya Alhamis inda ta sanar da mutan kasar cewa Shugaban kasar ya mutu a Barcelona.

A zahiri dai shekaranjiya Alhamis ne aka yi bukin cika shekaru takwas da mutuwar Mahaifin Ali Bongo wato Omar Ali Bongo wanda yam utu a Barcelona a ranar 8 ga watan shida na shekara ta 2009 bayan kwashe shekaru kusan 40 yana bias madafun iko.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.